Har yanzu tsuguni bata kare ba a game da batun gayyatar
shugaban hukumar kwastan ta kasa kanar Hamid Ali, mai ritaya zuwa majalisar
dattawa, domin sanata Ali Ndume ya ce yana da niyyar shigar da kara a kansa.
Wata sabuwa! Sanata Ndume zai maka hukumar kwastam kotu
Wata sabuwa! Sanata Ndume zai maka hukumar kwastam kotu
Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Sanata Ali
Ndume, ya bayyana cewa yana da niyyar shigar da karar shugaban hukumar kwastan
dinne a sakamakon wata sabuwar doka da shugaban ya bullo da ita wadda ta bukaci
biyan kudin futo kan dukkan motocin da ke cikin kasar komai tsufansu.
Sanata Ndume, ya bayyana cewa wannan doka da shugaban
hukumar kwastan ya bullo da ita ta sabawa alkawarin da suka yiwa al’ummar
Najeriya, ta dalilin haka ne Ndume, ya ce yayi niyyar kai shugaban kotu a
madadin jama’ar kasa.
Ya kuma kara da cewa ‘yan majalisar dattawan sun kauce,
domin a maimakon su yi abin da ya dami jama’a, sai suka raja’a kan maganar sa
kayan sarki, kuma daya daga cikin abinda bai amince da shi ba, shine yadda wasu
suka mayar da majalisar tamkar fadar wani da wani.
Da dama daga cikin dattawan suna ganin yadda aka mayar da
majalisar tamkar fadar Saraki da Dino, kuma ya kamata su dauki mataki akan wasu
abubuwa da ke gudna a majalisar amma sun yi kunnen uwar shegu wai da sunan a
zauna lafiya.
Shi kuwa Sanata Kabiru Marafan Gusau, ya ce yana matukar
goyon bayan da majalisa ta dauka akan shugaban hukumar kwastan din, domin idan
an duba da kyau, majalisar dattawa aikinta ne.

Post a Comment Blogger Facebook